Shugaban Kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu ya ce zai baiwa 'yan wasan Super Eagles ta Najeriya gudummawar dalar Amurka 500,000 da yayi alkawari duk da rashin nasarar da suka yi a hannun Morocco a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON).
A jiya Laraba ne Najeriya ta sha kashi a hannun Morocco da ci 4-2 a bugun fenariti, wanda hakan yasa ta kasa tsallakewa zuwa wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka.
Wasan dai ya kare ne babu ci bayan mintuna 120, Inda aka yi bugun daga kai sai mai tsaron gida, Samuel Chukwueze da Bruno Onyemaechi ne suka barar wa Najeriya da kawllayen, wanda hakan ya sa Najeriya ta yi rashin nasaran a hannun masu masaukin baki Morocco.

0 Comments:
Post a Comment