Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da kashe mutane hudu tare da kona shaguna da ‘yan ta’adda suka yi a jihar.
‘Yan ta’addan sun kai farmaki kauyen Damala da ke gundumar Woko a karamar hukumar Borgu a ranar Asabar din da ta gabata, a wani harin da suka kai da sanyin safiyar ranar, lamarin da ya haifar da firgici a yayin da mazauna garin suka ruga ta hanyoyi daban-daban domin neman tsira.
Wata majiya a yankin ta ce an kuma sace wasu mutanen da ba a bayyana adadinsu ba yayin harin.
.webp)
0 Comments:
Post a Comment