Jumhuriyar musulci ta Iran ta zartar da hukuncin kisa kan wani mutum da ake zargi da yi wa Isra'ila leken asiri.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya ruwaito cewa, ƙasar Iran ta zartar da hukuncin kisa kan wani mutum da ake zargi da yi wa Isra’ila leken asiri a yau Larabar, inda ta bayyana sunan sa da Hamidreza Sabet Esmaeilipour.
Kasar Iran dai ta dade ta na takun saka da yakin buya tsakanin ta da Isra'ila, Inda ta sha zartar da hukuncin kisa kan mutane da dama da ta samu da alaka da hukumar leken asirin Isra'ila, Mossad.

0 Comments:
Post a Comment