Hatsarin jirgin sama a India yayi sanadin mutuwar mataimakin babban ministan jihar Maharashtra.

Hatsarin jirgin sama a India yayi sanadin mutuwar mataimakin babban ministan jihar Maharashtra.

Hatsarin jirgin sama a India yayi sanadin mutuwar mataimakin babban ministan jihar Maharashtra.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Kasar India ta sanar da cewa, mataimakin babban ministan jihar Maharashtra, Ajit Pawar, ya mutu a yau Laraba, tare da wasu mutane hudu a cikin jirginsa da yayi hadari.

Kafafen yada labaran ƙasar sun ce Pawar, wanda ya fito daga manyan gidajen siyasa, yana kan hanyarsa ne ta zuwa yankinsa domin sanya ido a zaben kananan hukumomi da za'a gudanar.

Biyu daga cikin hadimansa da ma'aikatan jirgin biyu suna cikin jirgin, in ji babban daraktan kula da zirga-zirgar jiragen sama.

"Babu wani da ke cikin jirgin da ya tsira," in ji sanarwar ta farko.

Pawar ya goyi bayan jam'iyyar Bharatiya Janata ta Firayim Minista Narendra Modi a gwamnatin jihar, inda ya jagoranci wani bangare da ya balle a shekarar 2023 daga jam'iyyar Nationalist Congress Party ta adawa.
Bidiyon ya nuna hayakin da ke tashi daga wasu tarkacen jirgin da ya kone a wani fili.

Kafofin yada labarai sun ce jirgin Pawar, wanda ya taso daga babban birnin kasuwancin ƙasar Indiya Mumbai, ya yi kokarin yin saukar gaggawa a yankin Baramati, mai tazarar kilomita 250 (kilomita 155), inda ya shirya yin katsalandan a zaben da za'a gudanar na kananan hukumomi.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: