Gwamnatin jihar Kano ta bayar da gudunmawar Naira miliyan 25 ga iyalan jami’an JTF guda biyar da suka rasa rayukansu a Lokacin wani artabu da 'yan ta'adda.

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da gudunmawar Naira miliyan 25 ga iyalan jami’an JTF guda biyar da suka rasa rayukansu a Lokacin wani artabu da 'yan ta'adda

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da gudunmawar Naira miliyan 25 ga iyalan jami’an JTF guda biyar da suka rasa rayukansu a Lokacin wani artabu da 'yan ta'adda.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sani Surajo Abubakar ya fitar a ranar Alhamis a madadin babban daraktan ayyuka na musamman na gidan gwamnatin Kano.

“Gwamnatin jihar Kano ta bayar da tallafin Naira miliyan 25 don tallafawa iyalan jami’an JTF guda biyar a lokacin da suke bakin aiki a yayin wani artabu da ‘yan bindiga a karamar hukumar Shanono,” in ji sanarwar.

Da yake gabatar da cek ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hedikwatar 3 Brigade na rundunar sojojin Najeriya da ke Barikin Bukavu, Yusuf ya ce sun yi wannan karimcin ne da nufin tallafa wa iyalan jaruman da suka mutu wadanda suka sadaukar da rayukansu a lokacin da lamarin ya faru.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: