Dan takarar mataimakin gwamnan a jam’iyyar APC a zaben 2023, Murtala Garo, ya yi maraba da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar APC mai mulki

Dan takarar mataimakin gwamnan a jam’iyyar APC a zaben 2023, Murtala Garo, ya yi maraba da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar APC mai mulki

Dan takarar mataimakin gwamnan a jam’iyyar APC a zaben 2023, Murtala Garo, ya yi maraba da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Garo ya bayyana sauya shekar gwamnan a matsayin ci gaba mai kyau na samun kwanciyar hankali na siyasa da ci gaba mai dorewa a jihar.
Garo, wanda kuma tsohon kwamishinan kananan hukumomi da masarautu ne ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Inda yace, matakin da Yusuf ya dauka ya nuna karewar siyasa da hangen nesa a daidai lokacin da Kano da Najeriya ke bukatar hadin kai da gudanar da mulki.

“Ina maraba da Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf a hukumance a cikin Jam’iyyar APC, wannan wani muhimmin mataki ne kuma abin yabawa a kokarinmu na ganin mun samar da daidaito a siyasance, samar da shugabanci da ya hada da ci gaba mai dorewa a Jihar Kano,” inji Garo.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: