Anyi wa saurayi da budurwa bulala 140 a bainar Jama'a Saboda samun su da laifin aikata zina da shan barasa a lardin Aceh na Ƙasar Indonesiya.
Sai dai budurwar ta suma bayan ta jure hukuncin bulalar da aka yi mata kafin daga bisani a dauke ta a motar marasa lafiya zuwa asibiti.
Wadannan hukuncin shine mafi tsanani tun bayan da yankin mai ra'ayin mazan jiya ya amince da shari'ar Musulunci.
An haramta yin jima'i tsakanin ma'auratan da ba su yi aure ba a yankin Aceh da sauran laifuka da suka saba da koyarwar musulunci, wuri daya tilo a Indonesia dake aiwatar da tsarin shari'ar musulunci.
Masu laifin mace da namiji, an buge su ne da wata bulala da ake kira rattan a bayansu a wani wurin shakatawa na jama'a yayin da jama'a da dama ke kallo, kamar yadda wakilin AFP a wurin a wurin ya ruwaito.

0 Comments:
Post a Comment