Tinubu ya canja Sunan Jami'ar Azare da sunan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Tinubu ya canja Sunan Jami'ar Azare da sunan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya canza sunan jami’ar gwamnatin tarayya ta kimiyar lafiya da ke Azare a jihar Bauchi da sunan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi. 

Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Asabar a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan babban malamin addinin Islama a Bauchi.

Ya jinjinawa irin sadaukarwar da marigayi sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi a tsawon rayuwarsa ga bautar Allah, da kuma al’ummar Nijeriya.

Ya siffanta Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin fitaccen malami, mai bin tafarkin da’a, kuma mutum ne wanda koyarwarsa ta gaskiya da rikon amana da kyawawan halaye suka yi tasiri ga al’ummomi a fadin kasar nan da duniya baki daya.

Shugaba Tinubu wanda ya isa filin jirgin sama na Abubakar Tafawa Balewa, da misalin karfe 4:50 na yamma, ya samu tarbar gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed da gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang da ministoci, da sauran manyan jami'an gwamnati da suka halarci taron.

Daga cikin ministocin da suka halarci taron har da Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, da Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, wadanda suka bi sahun sauran manyan baki wajen tarbar shugaban.

Mambobin tawagar shugaban kasar sun hada da kakakin majalisar wakilai Tajuddeen Abbas, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni da sauransu.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: