'Yan bindiga sun kai hare-hare a jihohin Kogi da Zamfara, inda suka kashe akalla mutane 3 tare da yin garkuwa da wasu mutune 15 a wani hari na baya-bayan nan a daidai lokacin da matsalar rashin tsaro ke kara ta’azzara a shiyyar Arewa ta tsakiya da arewa maso yammacin Najeriya.
A jihar Kogi, ‘yan bindigan sun kaddamar da hare-haren ne a kan al’ummar karamar hukumar Kabba/Bunu, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla biyu tare da yin awon gaba da wasu da dama.
Shugaban karamar hukumar Barista Zacheus Dare Michael ya yi Allah wadai da hare-haren, inda ya jajantawa wadanda harin ya rutsa da su, ya kuma yi alkawarin kara hada kai da jami’an tsaro domin ganin an sako wadanda aka sace tare da dakile ‘yan fashi a yankin.
A halin da ake ciki kuma a jihar Zamfara ‘yan bindiga sun kai hari ne a kauyen Fananawa da ke karamar hukumar Bukuyum a daren ranar Asabar, 20 ga watan Disamba, 2025, inda suka kashe mutum daya, suka raunata wani, tare da yin garkuwa da akalla mutane biyar.
Wata majiya ta rawaito cewa maharan sun fara kai farmaki ne tun daga magriba har zuwa wayewar gari, yayin da rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da sace mutane biyar tare da tura jami’an ceto wadanda aka sacen.

0 Comments:
Post a Comment