Gwamnan Kaduna ya rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2026 na naira N985.9bn, inda ya ware kashi 25% a fanni ilimi.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya rattaba hannu a kan kasafin kudin shekarar 2026 na naira biliyan ₦985.9bn, inda bangaren ilimi ya samu kaso mafi tsoka na kashi 25 cikin 100 na kasafin kudin.
Gwamnan ya rattaba hannu kan kasafin ne a yau Litinin a zauren majalisar dake gidan Sir Kashim Ibrahim, Kaduna, inda ya bayyana kasafin kudin a matsayin wani abin da ke nuni da kudirin gwamnatinsa na tabbatar da nasarorin da aka samu tare da kafa ginshikin ci gaba mai dorewa.
A cewar Gwamnan, kasafin kudin na 2026, wanda aka yi wa lakabi da “Budget of Consolidation of Transformation for Inclusive Development,” ya ba da fifikon saka hannun jari da nufin bunkasa ci gaba a fadin jihar.
Da yake ba da Cikakken bayana game bangarorin kasafin kudin, gwamna Uba Sani ya ce an ware kashi 25 cikin 100 na kasafin kudin ga fanni ilimi, saboda muhimmiyar rawar da yake takawa wajen bunkasa cigaban dan Adam.
"Mun yi imanin cewa ilimi shine ginshikin aiki mafi karfi don karya talauci da kuma tabbatar da makomar 'ya'yanmu," in ji shi.
_1.webp)
0 Comments:
Post a Comment