Jami'an tsaron hadin Kai don yaki da 'yan ta'adda sun yi nasaran kama wasu motocin daukar kaya guda biyu da ake zargi za su kaima 'yan ta'addar ISWAP ne a jihar Borno.
Jami’in yada labarai na rundunar hadin gwiwa na Operation Hadin Kai, Laftanar Kanar Sani Uba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya Juma’a.
A cewarsa, kayayyaki da ke cikin motocin sun hada da, tayoyin mota guda 31, gare-garen taya 23, kekunan hawa biyu, buhun fulawa 2, buhunan gawayi guda biyar, buhunan doya guda 34, barguna rufa biyu, nailan guda biyu na garri, wayoyin salula guda 6, na'uran cajin waya (power bank) 2, da wasu kudaden Kasashe daban-daban.
Sani ya ce an gudanar da aikin ne biyo bayan sahihan bayanan sirri da su ka samu, inda aka sanar da hedkwatar rundunar game da jigilar kayan daga garin Dapchi a jihar Yobe zuwa yankin Magumeri a jihar Borno.
“Sakamakon binciken da aka yi cikin gaggawa, shine aka tura sojoji domin su tare motocin a kan hanyar ta zuwa jihar borno.
Ya kara da cewa, direbobin da su ka yi jigilar kayayyakin tare da kayayyakin da aka kwace, a halin yanzu suna hannun sojoji domin ci gaba da yi musu tambayoyi domin sanin girman hannunsu a laifin da kuma bayar da goyon bayan binciken da ake yi na yaki da ta’addanci.
"Wannan nasarar da aka samu ya nuna tasirin ayyukan leken asiri da kuma ci gaba da hadin gwiwa tsakanin sojoji da abokan tsaro na cikin gida wajen dakile hanyoyin sadarwa tsakanin 'yan ta'adda," in ji shi.
Ya kuma ba da tabbacin cewa, sojojin za su ci gaba da jajircewa wajen hana ‘yan ta’adda ‘yancin walwala, da yanke musu kayayyaki, da kuma tabbatar da tsaron ‘yan kasa masu bin doka da oda a fadin Arewa maso Gabas.

0 Comments:
Post a Comment