Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya amince da tsawaita shekarun ritayan malamai a jihar zuwa Shekaru 65.
Domin karfafa fannin ilimi a jihar Kaduna, Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya amince da inganta yanayin walwalar malaman jihar tare da tsawaita shekarun ritaya daga Shekaru 60 zuwa shekaru 65 a fadin jihar.
Matakin wanda zai fara aiki tun daga ranar 1 ga Agusta, 2025, yai tsawaita wajabcin shekarun ritayar malamai daga shekaru 60 zuwa 65, wanda hakan ke nufin shekarun aiki zai tashi daga 35 zuwa shekaru 40.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Mallam Ahmed Maiyaki ya fitar a ranar Juma’a, ya ce malaman da aka tura aiki a yankunan karkara da wuyar zuwa, za su samu alawus na musamman na aiki a can.
A cewarsa, amincewar ta yi daidai da dokar da ta dace da shekarun ritayar malamai a Najeriya, 2022, da Majalisar Dokoki ta kasa ta kafa, wadda ta kebe malamai daga matakin ritaya na aikin gwamnati na shekaru 60 ko 35, tare da sanin muhimmancin rawar da suke takawa wajen ci gaban kasa.
Kwamishinan ya ce, "Shawarar ta nuna kwazon Gwamna Uba Sani na inganta jin dadin ma'aikata da kuma farfado da fannin ilimi."

0 Comments:
Post a Comment