Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya sanar da kulla yarjejeniyar iskar gas ta dalar Amurka biliyan 35 da Masar a daidai lokacin da Amurka ke yunkurin gudanar da wani taro tsakanin shugabannin kasashen biyu.
A cikin wata sanarwa da aka watsa ta gidan talabijin, Netanyahu ya yaba da yarjejeniyar a matsayin "yarjejeniyar iskar gas mafi girma a tarihin Isra'ila."
Ya ce an kiyasta yarjejeniyar a kan shekel biliyan 112 (kimanin dalar Amurka biliyan 34.6).
Yarjejeniyar ta shafi kamfanin makamashi na Amurka Chevron kuma zai samar da iskar gas ga Masar.
"Wannan yarjejjeniyar ta kara karfafa matsayin Isra'ila a matsayin mai karfin makamashi a yankin kuma tana taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankinmu.
Tana karfafa wa sauran kamfanoni gwiwa su zuba jari a aikin hako iskar gas a cikin ruwan tattalin arzikin Isra'ila," in ji Netanyahu.
A cewar wata majiyar Isra’ila da ke da masaniya kan lamarin, Isra’ila ta jinkirta amincewa da yarjejeniyar a hukumance na tsawon watanni, inda daga karshe ta koma kan matsin lamba daga gwamnatin Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump na kokarin shirya wani taro tsakanin Netanyahu da shugaban Masar Abdel Fattah el-Sisi yayin da yake ci gaba da kulla yarjejeniyar zaman lafiya a yankin domin fadada yarjejeniyar Abraham.
Masar ta ce yarjejeniyar iskar gas da Isra'ila ta kulla ta kasuwanci ce, wadda aka kulla ta kan tattalin arziki da zuba jari kawai, ba tare da wani dalili na siyasa ba.
_3.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment