kisan kare dangi a Najeriya ba na addini kaɗai ba ne

kisan kare dangi a Najeriya ba na addini kaɗai ba ne

KISAN KARE DANGI A NAJERIYA BA NA ADDINI KAƊAI BA NE.

Tun daga shekarar 2009, gwamnatin Najeriya ta kashe tiriliyoyin kudi wajen sayen makamai, gudanar da ayyukan soji, taimakon tsaro daga ƙasashen waje da shirye-shiryen yaki da ta’addanci. Duk da waɗannan manyan kashe–kashen kudi, har yanzu ana kashe mutane ba ƙaɗan ba, ana yi wa mata fyade, ana sace mutane, kuma miliyoyin ‘yan kasa sun rasa gidajensu. Ayyukan rashin tausayi da ake yi sun kai matsayin kisan kare dangi, kuma sun shafi Musulmi da Kirista. Boko Haram da ISWAP sun addabi yankin Arewa maso Gabas; Fulani makiyaya masu dauke da makamai sun addabi Arewa ta Tsakiya; a Arewa maso Yamma kuwa, ‘yan bindiga, ISWAP da Laukurawa sun kashe Musulmai masu rinjaye. Duk da haka, gwamnatin Najeriya ta kasa cika mafi asalin hakkin ta: kare rayukan ‘yan kasa.

A kowane lokaci da aka yi kisar jama’a, gwamnati tana maimaita irin kalaman nan na yau da kullum: “Muna Allah wadai,” “Mun dauki mataki,” “Mun ci nasara akan ‘yan ta’adda,” ko “Muna amfani da dabarun kinetic da non-kinetic.” Amma gaskiyar da ke faruwa a fagen da abin ke aukuwa ta sabawa maganganun nan. Kowane lokaci da gwamnati ta kara propaganda, ‘yan ta’adda sukan kara karfi da jarumtaka. Sau da dama gwamnati ta yi alkawarin fallasa sunayen masu daukar nauyin ta’addanci, amma har yanzu an ki bayyanawa. Wannan ya haifar da shakku cewa akwai hadin baki ko sakaci a mafi girman matakai. Wannan ne ya sa ake cewa: Muryar na kama da ta Yakubu, amma hannun na Esau.

Akwai hujja karara cewa ana kashe Kiristoci da gangan a Najeriya. Masu aikata hakan sun hada da tsattsauran ra’ayin addinin Islama da kuma Fulani makiyaya masu makamai, wadanda dalilinsu ya samo asali daga akidar addini. Haka kuma, akwai kisan kiyashi akan Musulmai, musamman a Arewa maso Yamma, inda Boko Haram, ISWAP da ‘yan bindiga ke kashe Musulmai wadanda suka ki bin akidar tsattsauran fahimta. Saboda haka, kisan kare dangi a Najeriya ba na addini kaɗai ba ne — na talakawa ne. Ana kashe wadanda ba su da kariya, wadanda gwamnati ta bari daga rahamar kaddara.

Maganganun da wasu shugabannin kasashen waje ke yi sun haifar da muhawara a cikin ‘yan kasa. A yanayi na al’ada, irin wannan barazana daga kasashen waje zai sa al’umma su hade don kare kasarsu. Amma yanayin tsananin talauci, harajin wahala, hauhawar farashi, da sakacin gwamnati wajen kare jama’a ya sa mutane sun rasa tabi da bangare. Duk kuwa da haka, idan matsin lamba daga waje zai sa gwamnati ta dauki tsaron rayukan ‘yan kasa da muhimmanci, to babu laifi a karbar duk wani abu da zai sa shugabanni su zama masu amana.

Sai dai mu ma ‘yan kasa muna da laifi a wannan kuskuren. Kungiyoyin farar hula, shugabannin addini da al’umma ba su shirya tsayuwa tsayin daka ba domin tilasta gwamnati ta dauki mataki. Shugabannin Kirista sun yi shiru; manyan fastoci sun fi mayar da hankali kan zaben 2027. Haka ma shugabannin Musulmi ba su fuskanci matsalar tsattsauran akida a cikin al’ummar su yadda ya dace ba. Idan wannan kisan kare dangi ya ci gaba, me ya saura daga Najeriya? Don haka, lokaci ya kai mu daina munafunci, mu koyi irin yadda sauran al’ummai ke tsayawa tsayin daka, mu rike hakkin mu na dan kasa, mu tilasta gwamnati ta dauki mataki.

Solomon Dalung LLM LLB, BL
Igbarman Otarok & Garkuwan Arewa
igbarman@gmail.com


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: