Shugaban Amurka Donald Trump ya isa kasar Masar domin taro game da kawo karshen yakin Gaza.
Bayan ya gabatar da Jawabi a majalisar dokokin Isra'ila, shugaban Amurka Donald Trump ya isa kasar Masar inda shugabannin kasashen duniya suka hallara domin taro akan yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.
Ana sa ran Trump zai tattauna da shuwagabannin larabawa game da yadda za'a kawo karshen yakin gaba daya da kuma sake gina zirin na Gaza.
Haka zalika a yau litinin Israi'la ta fara sakin Falasdinawa da ake tsare da su a gidajen yari na Isra'ila bayan da kungiyar Hamas ta sako daukacin fursunonin Isra'ila 20 da ke tsare a zirin Gaza a wani bangare na yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Tun bayar sanar da amincewar bangarorin biyu game da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza Falasdinawa ke ci gaba da komawa sauran gidajensu a arewacin Gaza yayin da ake bukatar agajin jin kai a cikin yankin da hare-haren bama-bamai Israi'la ya daidaita.
Yakin Isra'ila a Gaza ya kashe akalla mutane 67,869 tare da raunata 170,105 tun daga watan Oktoba na shekarar 2023. A kalla mutane 1,139 aka kashe a Isra'ila yayin harin da Hamas takai a ranar 7 ga Oktoba, 2023, kuma an kama kusan mutane 200.

0 Comments:
Post a Comment