Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya gabatar da sunan Amupitan a yayin taron majalisar a fadar shugaban kasa, Abuja, domin cike gurbin da Farfesa Mahmood Yakubu ya bari, wanda ya rike mukamin shugaban INEC din daga 2015 zuwa Oktoba 2025.
A cewar wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, a yau Alhamis, 9 ga watan Oktoba, Tinubu ya bayyana cewa, Amupitan, Farfesa a fannin shari’a daga jihar Kogi a yankin Arewa ta tsakiya, shine mutum na farko da aka zaba daga jihar domin neman mukamin.
Ya kuma bayyana wanda aka nada a matsayin "Wanda baya siyasa kuma wanda ya cancanta” don jagorantar hukumar zabe.

0 Comments:
Post a Comment