Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta kaddamar da bincike a kan Farfesa Saleh Abdullahi Usman, Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), kan wasu makudan kudade da suka shafi ayyukan Hajji na 2025.
A cewar majiyoyi, Usman ya gabatar da kansa a hedikwatar EFCC da safiyar jiya Laraba don amsa gayyatar da aka yi masa.
Daga baya an sake shi bisa belin gudanarwa amma ana bukatar ya kai rahoto ga Hukumar a kullum yayin da ake ci gaba da bincike.
Binciken ya biyo bayan zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake ta tafkawa a cikin Hukumar, da suka hada da karkatar da wasu makudan kudade da suka kai sama da Naira biliyan 50.
Takamammen zarge-zargen sun hada da amfani da Naira biliyan 25 ba tare da izini ba ga tantunan Masha’ir, da kashe Naira biliyan 7.9 wajen Samar da gidajen gaggawa da kuma Naira biliyan 1.6 na kudaden tafiye-tafiye ga iyalan manyan jami’ai.

0 Comments:
Post a Comment