Kwamitin hadin gwiwa na majalisar dokokin Najeriya kan sake duba kundin tsarin mulkin kasar ya amince da kirkiran sabbin jihohi shida, daya a kowanne shiyyar siyasar Najeriya, a wani bangare na kudurin da ta yi na sake duba kundin tsarin mulkin kasar.
Idan har aka amince da kudurin a gaban zauren majalisun kasar, adadin jihohin da Najeriya ke da su zai tashi daga 36 zuwa 42, inda yankin Arewa maso Yamma zai samu takwas, sannan Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya, Kudu maso Yamma, Kudu maso Kudu na da bakwai kowanne, sannan Kudu maso Gabas na da shida.
An cimma wannan matsaya ne a yayin wani taro na kwanaki biyu da aka gudanar a Legas daga ranar Juma’a zuwa Asabar.
Kwamitin Wanda mataimakin Shugaban majalisar Dattijai, Onarabul Barau Jibrin ya Jagoranta ya kuma yanke shawarar kafa wani karamin kwamiti da zai tantance takamaiman wuraren da za a kirkiro sabbin jihohi shida daga cikinsu.
An nada Mai tsawatarwa na Majalisar Dattijai Tahir Monguno (APC, Borno ta Arewa), don ya jagoranci karamin kwamatin.
Ana sa ran mataimaka shugabannin majalisun biyu, mataimakin shugaban majalisar dattijai, Onarabul Barau Jibrin, da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Onarabul Ben Kalu, za su gabatar da kudurorin kwamitin a lokacin da ‘yan majalisar suka dawo zama a man gaba.
Sannan za a yi muhawara kan matsayar da kwamitin ya cimma, inda mambobin za su kada kuri'a don amincewa ko kin amincewa da hakan.
_2.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment