A kalla mutane hudu ne aka kashe a zanga-zangar adawa da sakamakon zabe a Kasar Kamaru.

A kalla mutane hudu ne aka kashe a zanga-zangar adawa da sakamakon zabe a Kasar Kamaru.

Mutane hudu ne suka mutu sakamakon arangamar da aka yi tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan madugun 'yan adawar Kamaru wanda ya yi ikirarin lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a baya-bayan nan, kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana gabanin bayyana sakamakon a hukumance a yau Litinin.

Issa Tchiroma, wanda ya kalubalanci mulkin Shugaba Paul Biya na tsawon shekaru 43 a zaben ranar 12 ga watan Oktoba, ya yi kira ga magoya bayansa da su yi zanga-zangar lumana a jajibirin sanarwar, duk da haramta taron jama'a.

Tchiroma ya ce ya samu kashi 54.8 cikin 100 na kuri'un da aka kada, sai dai galibin masu sharhi na ganin Biya mai shekaru 92 zai sake lashe zabe karo na takwas a tsarin da masu sukarsa suka ce ana tafka magudi.

A birnin Douala mafi girma a Kamaru, gwamnan yankin ya ce masu zanga-zangar sun "kai hari" wata birgediya ta Jandarma da ofisoshin 'yan sanda a gundumomi biyu ranar Lahadi.

Samuel Dieudonne Ivanaha Diboua ya ce: “Mutane hudu cikin rashin tausayi sun rasa rayukansu, ya kuma kara da cewa jami’an tsaro da dama sun samu raunuka.

Masu zanga-zangar a wurin sun nuna wa manema labarai na tashar AFP bawon harsasai da suka ce sun tattara bayan da jami’an tsaro suka yi harbi a kusa da jami’an Jandarma.

An fara harbe-harbe da "harsashin gaske" bayan hayaki mai sa hawaye, inji wani mai zanga-zangar da ya shaida wa kafar watsa labarai na AFP bisa sharadin sakaya sunansa.

"Sun yi harbi, mutane uku, gawarwaki uku suka fadi a gabanmu," in ji shi.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: