Kungiyar malaman jami’o’in gwamnati, ASUU, ta dakatar da yajin aikin gargadi na makwanni biyu da ta shelanta a makon jiya a dukkan jami’o’in gwamnati na kasar nan.
Kungiyar ta sanar da dakatarwar ne a ranar Laraba a wani taron manema labarai da ta gudanar a hedikwatar ta da ke Abuja.
Shugaban ASUU, Chris Piwuna, wanda yayi jawabin da aka shirya a gaban manema labarai, ya bayyana cewa dakatar da yajin aiki ya biyo bayan sa hannun majalisar dattawa kasar ne tare da wasu ‘yan Najeriya masu kishin kasa.
Ya kuma kara da cewa Majalisar zartaswar kungiyar ta kasa ta baiwa gwamnatin tarayya wata guda domin magance duk alkawuran da ake takaddama a kai.
_1.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment