Bisa Alkaluman da babban bankin Najeriya CBN ya fitar sun nuna cewa darajar Naira akan dalar Amurka ya karu a ranar Talata daga N1,463.45 idan aka kwatanta da yadda aka canja dalar daga N1,465.29 a ranar Litinin.
Wannan yana nufin cewa darajan kudin kasar ya samu karuwar N1.8 akan kowace dala $1 a kasuwar hada-hadar kudade ta FX a hukumance.
Sai dai a kasuwar canji ta bayan fage farashin bai canja ba akan yadda aka sayar da dalar Amurka$1 akan N1,500 a Ranar litini.
_2.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment