Kasar Morocco ta samu nasaran lashe gasar cin kofin Duniya na yan kasa da Shekaru 20 bayan da ta doke kasar Argentina da ci 2-0 a wasan karshe.
Nasaran da Morocco ta samu ya zama na biyu a tarihin Africa bayan nasaran da Ghana ta yi na lashe gasar a Shekarun 2009.
Dan wasan Morocco Yassir Zabiri Wanda ke taka leda a Kungiyar kwallon kafar FC Famalicao dake kasar Portugal ne ya zura duka kwallayen tun kafin a tafi hutun rabin lokaci.
_1.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment