Shahararren dan jaridan nan dan Kasar Sin (china) mai magana da harshen hausa, Murtala Zhang ya gana da ministan tsaron Najeriya, Badaru a lokacin ziyaransa a kasar china.
A wani Dan Takaitaccen bidiyo da Murtala Zhang ya saki a shafinsa na Facebook ya baiyana jin dadinsa ga ziyaran na ministan inda har ya tambaye shi game da ingancin maganar da yake yi da harshen hausa, Kuma ministan ya ce mashi lallai ya iya magana da harshen hausa sosai.
Ministan yayi masa rahan cewa sai dai baka iya Karin magana ba, inda nan take Murtala Zhang din yace mashi zai iya biyu zuwa uku.
Latsa wannan bidiyon dake kasa domin sauraron cikakkiyar tattaunawarsu.
_1.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment