El Clasico: Za'ayi Karan batta tsakanin Real Madrid da Barcelona karo na 262 a tarihi

El Clasico: Za'ayi Karan batta tsakanin Real Madrid da Barcelona karo na 262 a tarihi

A yau ne manyan kungiyoyin kwallon kafar Real Madrid da Barcelona zasu kece raini a wasan Laliga mako na 9, karawar da ake wa lakabi da "El clasico".

Manyan kungiyoyin sun kasance abokan hamayya tun tsawon lokaci inda suka fafata a karawa 261 a dukkanin wasannin.

A cikin karawa 261 da kungiyoyin suka yi Real Madrid ce ke kan gaba a samun nasara, inda ta doke Barcelona sau 105 yayin da Barcelona ta yi nasara akan Real Madrid din sau 104 , sannan suka yi chanjaras sau 52.

A gasar La Liga kungiyoyin biyu sun kara da juna sau 190, inda Real Madrid ta samu nasara a wasanni 79, Barcelona ta samu nasara sau76, sannan suka yi chanjaras 35 a fafatawar.

Sai dai a wannan fafatawar wacce 'yan kallo ke jiran ganin yadda zata kaya, zamu iya cewa lokaci ne kadai zai iya tabbatar mana da Wanda zai samu nasara, kasantuwar dukkanin kungiyoyin suna da kwarewa ta mu musamman da salon wasa.

A halin yanzu dai Real Madrid ce ke jagorancin teburin na Laliga da maki 24 yayin da Barcelona ke bin ta da maki 22.

Za'a fafata wannan wasan ne a filin wasa na Santiago Barnebao dake birnin Madrid da misalin karfe 4:30pm agogon Najeriya da Nijar.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: