Iran ta zartar da hukuncin kisa kan daya daga cikin manyan 'yan leken asiri' ga Isra'ila.
Kasar Iran ta zartar da hukuncin kisa kan wani mutum mai suna Bahman Choubi-asl a yau Litinin, inda ta ce wanda ake tuhuma yana daya daga cikin masu leken asiri mafi muhimmanci ga Isra'ila a Iran.
Iran ta zartar da hukuncin kisa kan mutane da dama a wannan shekaran wadanda ta zarga da alaka da hukumar leken asiri ta Mossad ta Isra'ila da kuma gudanar da ayyukanta a kasar.
%20(3)_1.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment