Iran ta harbo jiragen yakin Isra'ila biyu, ta kuma kama matukin jirgin - inji Rundunar tsaron kasar.

Iran ta harbo jiragen yakin Isra'ila biyu, ta kuma kama matukin jirgin - inji Rundunar tsaron kasar.

Iran ta harbo jiragen yakin Isra'ila biyu, ta kuma kama matukin jirgin - inji Rundunar tsaron kasar.

Rundunar Sojin saman Iran sun sanar a yammacin jiya Juma'a cewa sun kakkabo jiragen yakin Isra'ila biyu tare da kame matukin daya daga cikin jiragen. 

A wata sanarwa da rundunar sojin saman ta fitar ta ce ta kama daya daga cikin matukan jirgi biyu, mace bayan an harbo jirginta. 

Ta dauki wannan aiki a matsayin "nasara" a kokarinta na tunkarar hare-haren Isra'ila da kuma "tabbatar da shirye-shiryen sojojin da suke yi na tunkarar duk wata barazana da ke tunkaran kasar." 

A daren ranar Alhamis ne dai dakarun Sojin saman Isra'ila suka kaddamar da hare-hare ta sama a cibiyoyin tashar makamin Nukiliyan kasar da wurare da dama a fadin kasar ta Iran, musamman Tehran babban birnin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama ciki harda manyan kwamandojin kasar uku.

Sai dai Iran din ta mayar da martani  a daren jiya juma'a inda tayi ruwa makamai masu linzami a biranan Jerusalem da Tel aviv.

Birnin Tel aviv babban birnin Israi'la bayan harin ramuwar gayyar da makami mai linzami da Iran tayi a daren juma'a.

Anga yadda hayaki da karan fashewar makami mai linzami ya turnike biranen a cikin daren, sai dai har zuwa yanzu hukumomin israi'lan ba su sanar da adadin wadanda suka rasa rayukansu a harin ramuwar gayyar Iran din ba.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: