Kasar Iran ta kaddamar da harin ramuwar gayya akan Israi'la bayan harin da Israi'lan ta kai cikin dare akan cibiyoyin tashar makamin Nukiliyan kasar.
Rundunar tsaron Israi'lan IDF ta sanar da cewa a kalla jirage marasa matuka 100 ne Iran ta harbo zuwa cikin Israi'la bayan kaimata hari a daren jiya akan cibiyoyin tashar makamin Nuclear kasar, sai dai basu bayar da rahoto game da barnan da harin yayin ba.
Harin na Iran martanani ne game da harin da Israi'lan ta kai mata a cikin daren jiya kan cibiyoyin tashar makamin Nuclear kasar wanda yayi sanadin rasuwar babban kwamadan dakarun juyin mulkin kasar Hossein Salami da wasu shugabannin sojoji da dama da suka hada da babban hafsan hafsoshin sojan kasar Manjo Janar Mohammad Bagheri da kuma akalla masana kimiyyar nukiliya guda biyu.
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana cewa Iran zata dau tsatstsauran martani, yayin da Kasashen yamma ke kiran Kasashen da su kai zuciya nesa.
Hukumar da ke sa ido kan makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa tashar nukiliyar Natanz da ke da tazarar kilomita 225 kudu da Tehran na daga cikin wuraren da aka kai harin.
Shima Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a gidan talabijin na Fox News cewa yana sane da shirin Isra’ila amma ya musanta cewa Amurka ta taka rawa a harin.
Masana harkokin siyasar Iran da dama sun sha alwashin cewa Iran za ta mayar da martani mai mahimmanci ga hare-haren da Isra'ila ta kai a daren jiya.
"Lokacin daukar fansa ya zo, kuma za a aiwatar da wannan ramuwar gayya ta kowace hanya," in ji Mohammad Bagher Ghalibaf, kakakin majalisar shawarar Musulunci ta Iran.
Janar Ali Fadavi, mataimakin babban kwamandan dakarun kare juyin juya hali (IRGC), ya ce "ana yin shirye-shirye masu mahimmanci don mayar da martani ga Isra'ila". Ya kara da cewa IRGC na kan "cikakkiyar lura" kuma ta shirya don ɗaukar fansa mai tsanani".
0 Comments:
Post a Comment