Harin da Iran takai cikin Israi'la ya hallaka mutum 8

Harin da Iran takai cikin Israi'la ya hallaka mutum 8

Hare-haren na zuwa ne bayan da sojojin Isra'ila suka yi ruwan bama-bamai kan farar hula da cibiyar makamashin Gas na kasar Iran, lamarin da ya haddasa tashin gobara a cibiyar ta Shahran da ke birnin Tehran. 

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hari kan wuraren ne wanda ke da alaka da shirin nukiliyar gwamnatin Iran". 

Kafofin yada labaran Iran sun ce hare-haren Isra'ilan sun kashe akalla mutane 80 tare da jikkata wasu 800 a cikin kwanaki biyun da suka gabata. 

Wadanda aka kashe sun hada da yara 20.

Sai dai zuwa yanzu babu cikakken rahoto game da yawan wadanda suka hallaka a bangaren Israi'lan tun bayan barkewar rikicin.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: