Dubun dubatar mutane ne suka yi dafifi a kan tituna a Tehran babban birnin kasar Iran, yayin da kasar ke gudanar da taron jana'izar kwamandojin soji, da masana kimiyyar nukiliya da kuma wasu fararen hula da aka kashe a hare-haren Isra'ila a farkon wannan wata.
Gidan Talabijin na kasar ya nuna hotunan mutanen da suke sanye da bakaken kaya, suna daga tutocin Iran da kuma rike da hotunan wasu da suka rasu a lokacin yakin a warin jana'izar wacce aka fara da misalin karfe 8 na safe (04:30 agogon GMT) a yau Asabar.
Hotunan da ke tsakiyar birnin Tehran sun nuna akwatunan gawa da aka lullube da tutocin kasar Iran da kuma dauke da hotunan kwamandojin da suka rasa rayukansu a lokacin yakin da kasar da gwabza da Israi'la.
A ranar 13 ga watan Yuni ne dai Isra'ila ta kaddamar da farmaki kan babbar abokiyar hamayyarta yankin gabas ta tsakiya, inda ta kashe wasu manyan jami'an sojin kasar ta Iran da jami'an kimiyyan Nukiliya, tare da kai hare-hare kan wuraren soji da cibiyoyin nukiliya a fadin kasar.
Iran ta mayar da martani da harin makami mai linzami kan Isra'ila, lamarin da yasa aka kwashe kwanaki 12 ana gwabza hare-haren tsakanin Kasashen.
Wanda daga karke sai da Kasar Amurka ta shigar wa kasar Israi'lan yakin inda Shugaban Amurka Donald Trump ya Kai hari kan cibiyoyin tashar makamin Nukiliyan Iran dake Fordow Isfahan da Natanz da jirgin yakin B-2 da nufin lalata shirin Nukiliyan Iran din Amma daga bisa hukumar leken asirin ta Amurka dake Pentagon ta fitar da bayanin cewa harin bai lalata tashoshin Nukiliyan Iran din ba lamarin da Trump din ya karyata, Yana mai cewa karya suke yi.
Kwana daya da Kai harin ne sai Shugaban na Amurka Donald Trump ya sanar da cewa Kasashen sun cimma yarjejeniyar tsagaiywuta a tsakanin Kasashen biyu.
0 Comments:
Post a Comment