Tarihin Sheikh Uthaimin
Assalamu alaikum ..malam ALLAH ya saka muku da alkhairi akan fadakarwar da ake mn ALLAH kuma yasa a mizani.mllm inada tmby kamar haka mllm shin sheikh ibn usaimin din nan dan wane kasace dan ALLAH a dan fadamun tarihin shi a takaice.ngd
:
*****
:
Wa'alaikumussalam warahamatullahi wabarkatuhu
Alhamdulillah mun gode bisa kyautata mana zato da kuke, dakuma addua Dare da rana:- kuma ALLAH yasaka muku da alheri!
..
Al-padilatul sheek Abu Abdallah Muhammad ibn Saalih ibn Muhammad ibn Sulayman ibn Abdurahaman shek Uthaymeen Al-Tamimi, wanda aka taqaita yakoma *Shek Muhammad bin salihul ussaimin*
.
An haifeshi 9 awatan March , 1925 dan garin Unaizah, (qasarsu kuma itace) Saudi Arabia.
.
Alhamdulillah rayuwan malan tayi albarka sosai da sosai, yasamu kula dakuma manyan malamai, irinsu shek binbaz da sauran su!
Malan ya rayu cikin ilmi yakuma koyar da ilmi, abisa fahintan sahabbai da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa, malan yana da'awa abisa manhajis salafiyya! Yayiwa musulunchi manya manyan ayyuakan alherai
.
Ya wallafa littafai, yayiwa wasu daga cikin littafan ibni taymiyya takhariji ya rage musu wahala ya sauqaqa, yayi ma wasu, ya karantar da littafan malamai da dama. Akasamu Audio su, aka medasu littafai, kusan haryanxu ana kan aikata haka, ya rike babban matsayi jamiar madina! Yakuma zama babban me bada fatawa aqasar aduniya baki daya
.
Kaman yadda nace "ya rayu cikin neman ilmi da bada ilmi" bedana ba harma, akan gadon asibiti inbeda lapiya, yana karantarwa !!
.
Yayi fama da yan shi'a da yan bidi'a kala kala, irinsu yan ikwan (muslim brother's), almajiran (sayid qutub) da yan tablik, da kwawarijawa (usama bin ladan) (anan dai kaman kuce yan boko haram) !! Alokacin yana raye dashi da makaman tansa, sun tsoratar da mutane dangane da sharrinsu, hakama shek bin baz ya tsoratar da kada abi 'yan bidia dasu muslim brother's, hakasu Sheek rabe bin hadi Almadakhali (hafuzahullah) haryau sunata fama dasu...
.
Malan ya karantar da dalubai dayawa, kuma yanada dalubai asassan duniya da dama, littafansa kuma sun yawaita, kuma sun shiga duniya "bansan wata qasa guda dayaba wanda basa amfanuwa da littafansaba, bugu da qari gomnati tayi ruwa da tsaki wajen yada littafan sa, kuma duk wanda ya karanta ze gane akwai fasaha dakuma saukin fahinta in sha ALLAHU
Sannan malan jinya yayi tazama ajalinsa, ba kashe shi akayi ba ko harbewa ba, sannan ya bar duniya idonsa, suna gani, ma'ana dai be makanceba.
:
Watarana yana tafiya shida dalibinsa amota, se sukaxo Rawun (Cros) danger ya tsayar dasu, se dalubin ya wuce be tsayaba, daga baya se malan ya fahinci, lalle dalubin ya taka doka, bayan anbiyosu! Da akaga malan ne, se akamar affuwa! seyaqi yadda da afuwan "ya tambayi kudin taran yabiya rabi, yace dalubin yabiya rabi" (saboda shi dalibin yataka doka, malan kuma yagani be hanashiba, shiyasa yace subiya rabi rabi). ALLAH yajiqan maza!
.
Akwai inda yake fada "ya wayi gari beda ko riyal daya a aljihunsa"
.
ALLAH ya kar6i rayuwan sa, awatan 6-5-2001, yabar duniya yanada shekaru 75 in sha ALLAHU, yanxu kimanin shekara 17 kenan da rasuwan sa
.
ALLAH yajiqansa da rahama yasa Aljanna ce makoma agaresa dashi da sauran malaman sunnah da mabiya sunnah. "wannan shine taqaiceccen abinda zan iya fada akan shi".
-Daga shafin Khulafa'un rashidun na Facebook.
0 Comments:
Post a Comment