Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bar ƙasar Saudiyya domin komawa Najeriya bayan kammala aikin Umrah na tsawon mako guda a birnin Makkah mai tsarki.
Jirgin shugaban ƙasar ya tashi daga filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke birnin Jeddah da misalin ƙarfe 5:13 na yammacin Laraba, agogon Saudiyya.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Mataimakin gwamnan yankin Makkah, Yarima Saud bin Mishaal bin Abdulaziz Al Saud, jakadan Najeriya a Saudiyya, Yakubu Gambo, da kuma babban jakadan ƙasar (Consul-General), Muazam Ibrahim Nayaya, na cikin manyan jami'an da suka raka shugaban ƙasar zuwa filin jirgin saman.
Kafin tashinsa, Tinubu ya gana na ɗan lokaci da mataimakin gwamnan a fadar baƙi ta masarauta da ke cikin harabar filin jirgin saman.
Shugaban ƙasar ya isa Saudiyya a ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata, inda ya gudanar da ibadu daban-daban, ciki har da aikin Umrah da dawafin ɗakin Ka'aba da ke cikin Masallacin Harami a Makkah.
Ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka fi daukar hankali a ziyarar shi ne lokacin da Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz Al Saud, ya ba Tinubu da tawagarsa damar shiga cikin ɗakin Ka'aba a ranar Lahadi, inda suka gudanar da raka'a biyu na nafila.
A yayin ziyarar, Tinubu ya yi addu'o'in samun zaman lafiya, tsaro, haɗin kai da wadata a Najeriya, tare da neman taimakon Allah wajen ba shi hikima da ƙarfi domin ci gaba da jagorantar al'ummar ƙasar.
Da yake magana da 'yan jarida bayan kammala aikin Umrah a ranar Juma'a, shugaban ƙasar ya bayyana cewa Allah ne kaɗai ke da ikon ƙayyade wanda zai jagoranci Najeriya.
Ya ce: "Allah ne kaɗai zai iya ƙayyade abin da mutum zai kasance, abin da zai zama da kuma makomar rayuwarsa."
A ranar Litinin, Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da bunƙasa Najeriya, yana mai cewa jajircewarsa wajen samar da wadata da ci gaban ƙasar na nan daram.
Haka kuma, ya nuna godiyarsa ga Sarki Salman da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, bisa kyakkyawar tarba da karamcin da suka nuna masa da tawagarsa, musamman damar da suka ba su ta shiga cikin ɗakin Ka'aba.
Ziyarar ta kuma jawo hankalin masu sharhi kan siyasa saboda lokacin da aka gudanar da ita, kasancewar ta zo ne kwanaki kaɗan bayan Tinubu ya ƙaddamar da kamfen ɗin neman sake zaɓensa a Kaduna a ranar 24 ga Oktoba, gabanin zaɓen shugaban ƙasa da aka tsara gudanarwa ranar 16 ga Janairu, 2027.
Daga cikin jami'an da suka kasance tare da shugaban ƙasar a jirgin dawowarsa Najeriya akwai Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, da gwamnonin jihohin Sokoto, Jigawa, Kaduna, Borno da Yobe, tare da wasu manyan jami'an gwamnati.
Tags
Labarai
