Abdul El-Sayed Ya Zama Musulmi Na Farko Da Aka Zaba Zuwa Majalisar Dattawan Amurka

Abdul El-Sayed Ya Zama Musulmi Na Farko Da Aka Zaba Zuwa Majalisar Dattawan Amurka

Dan siyasar jam’iyyar Democrat, Abdul El-Sayed, ya kafa tarihi bayan samun nasara a zaben tsakiyar wa’adin shugabancin Amurka na shekarar 2026 a jihar Michigan, inda ya zama Musulmi na farko da aka zaba zuwa Majalisar Dattawan kasar (US Senate).

Dan shekaru 42 da haihuwa, wanda Ba’amurke ne mai asalin kasar Masar, ya doke tsohon dan majalisar wakilan Amurka na jam’iyyar Republican, Mike Rogers, a zaben da aka gudanar ranar Talata, inda ya lashe kujerar da Sanata Gary Peters mai ritaya ya bari.

Da yake mayar da martani kan nasarar da ake hasashen ya samu, El-Sayed ya bayyana godiyarsa, yana mai cewa samun damar zama zababben Sanata abin alfahari ne da kuma babban matsayi a gare shi.

A yayin jawabin da ya gabatar ga magoya bayansa a daren Talata, ya tuna yadda ya saba amfani da kalmar Musulunci ta “Insha Allah”, wadda ke nufin Allah Ya so, a duk lokacin da yake magana kan yiwuwar samun nasara a zaben.

Sai dai bayan hasashen nasararsa, ya ce lokaci ya yi da zai maye gurbin kalmar da “Alhamdulillah”, wadda ke nufin godiya ta tabbata ga Allah.

Ya ce: “Sunana Abdulrahman Mohamed Sayed, kuma ina matukar alfahari da girmamawa bisa tsayuwa a nan a matsayin zababben Sanatan ku daga babbar jihar Michigan.”

Nasarar El-Sayed ta biyo bayan zaben fidda gwani na jam’iyyar Democrat da aka gudanar a watan Agusta, inda ya doke ‘yar majalisar wakilai, Haley Stevens, domin samun tikitin takarar jam’iyyar.

Kafin shiga takarar kujerar Sanata, El-Sayed ya taba rike mukamin jami’in kula da harkokin lafiyar jama’a, sannan ya yi fice a harkokin siyasar jihar Michigan.

Ana sa ran zai fara aiki a hukumance a watan Janairun 2027, lokacin da sabuwar Majalisar Dokokin Amurka za ta fara zama.

Zabensa ya zama wani muhimmin tarihi a siyasar Amurka, musamman wajen kara samun wakilcin Musulmi a cikin manyan hukumomin gwamnatin kasar.

Muhammad Ahmad

manufar mu itace muga mun da dada ma duk wani ma,abuci jin harshen hausa a duk inda yake aduniya.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form