Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Rogo a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Fanka, bayan sun kashe mutane biyu a wani sabon hari da suka kai a yankin.
Rahotanni sun ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na dare ranar Litinin, lokacin da ‘yan bindigar suka mamaye yankin tare da bude wuta, lamarin da ya sa mazauna garin suka tsere domin tsira da rayukansu.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa mutanen biyu da aka kashe sun yi ƙoƙarin hana ‘yan bindigar yin garkuwa da Fanka, amma suka kasa saboda maharan na ɗauke da manyan makamai.
Harin ya zo ne kasa da sa’o’i 24 bayan da wasu ‘yan bindiga suka kashe shugaban Jam'iyyar APC na unguwar Rantan da ke ƙaramar hukumar Bebeji, Alhaji Garba Buba, da wani mazaunin yankin mai suna Sulaiman Zunduma.
Abubuwan da suka faru sun ƙara haifar da fargaba game da matsalar tsaro a jihar Kano, yayin da ake samun hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a sassa daban-daban na jihar.
A baya, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari garin Chiromawa da ke ƙaramar hukumar Garun Mallam, inda suka yi garkuwa da Sarkin Noman Kano, Alhaji Yusif Nadabo. Daga baya jami’an tsaro da mazauna yankin sun yi nasarar kuɓutar da shi, yayin da mutane uku suka samu raunuka.
Hare-haren da aka kai a Rogo, Bebeji da Garun Mallam sun faru cikin kimanin sa’o’i 72, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin al’umma.
A ranar Litinin, karamin Ministan Tsaro, Bello Muhammad Matawalle, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin samar da wani tsari na tsaro da kare ƙasa na tsawon shekaru biyar, sakamakon hare-haren baya-bayan nan da ake samu a Kano.
A halin yanzu, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta fara bincike kan hare-haren, yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin gano tare da kama waɗanda suka aikata laifukan.

0 $type={blogger}:
Post a Comment