Mutane 24, mafi yawansu matasa ne, suka mutu a yankin ƙaramar hukumar Odigbo da ke jihar Ondo, bayan da suka sha wata barasa na gida da ake zargin akwai sinadaran dake haddasa guba.
Wasu daga cikin mutanen da lamarin ya rutsa da su suna karɓar magani a asibitoci, yayin da jami’an lafiya ke gudanar da bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar.
Rahotannin farko sun nuna yiwuwar kasancewar methanol, wani sinadari mai guba, a cikin wasu daga cikin abubuwan shan (barasan) da aka yi amfani da su. Sai dai ana ci gaba da gudanar da gwaje-gwajen dakin bincike domin tabbatar da hakan.
Saboda wannan lamari, ƙaramar hukumar Odigbo ta sanya haramcin wata ɗaya kan sayarwa da shan giya da ake sarrafawa a gida a yankin.
Hukumomi sun gargadi masu sayarwa ko rarraba irin waɗannan abubuwan sha cewa za a iya kama su tare da gurfanar da su a gaban kotu idan suka karya dokar.
Lamarin ya haifar da fargaba da tashin hankali tsakanin mazauna yankin. Matasa sun gudanar da zanga-zanga suna neman hukumomi su ɗauki matakan gaggawa domin hana ƙarin asarar rayuka.
Sarkin Odigbo, Oba Rufus Akinrinmade, ya roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu, tare da tabbatar musu cewa ana ƙoƙarin gano musabbabin mutuwar tare da samar da mafita.

0 $type={blogger}:
Post a Comment