Jami'an tsaron Isra’ila sun Kashe wani bafalasdine a birnin Kudus.

Jami'an tsaron Isra’ila sun Kashe wani bafalasdine a birnin Kudus.

Rundunar tsaron Isra’ila ta harbe tare da kashe wani Bafalasɗine mai shekaru 33 a kusa da Ƙofar Damascus da ke birnin Kudus ranar Juma’a, 4 ga Satumba, 2026, bayan da ta yi zargin cewa mutumin ya yi yunkurin daba wa wani jami’in tsaron kan iyaka wuka.

Majiyar Falasɗinawa ta bayyana mutumin da sunan Ibrahim al-Hendi, mazaunin unguwar Beit Hanina da ke Gabashin Kudus.

Lamarin ya faru ne yayin da sojojin Isra’ila ke ci gaba da gudanar da samame a yankunan Yammacin Kogin Jordan da Falasɗinawa ke zaune. Hukumomin Isra’ila sun ce sun kama wasu Falasɗinawa a Qabatiya, yayin da wasu 10 kuma aka kama a wani samame da aka gudanar na tsawon sa’o’i 48 a Nablus.

A wani labarin makamancin haka, sojojin Isra’ila sun hana wasu masu rajin zaman lafiya kusan 100 kai abinci, ruwa da magunguna ga iyalan Falasɗinawa uku da ke Qusra, kudancin Nablus.

Iyalan sun shafe kwanaki 28 suna cikin matsanancin hali, bayan da wasu ‘yan share wuri na Isra’ila suka killace gidajensu tare da hana su samun kayayyakin masarufi.

Kungiyar Peace Now ta Isra’ila ta ce jami’an sojin sun fara hana masu fafutukar shiga yankin, daga bisani suka bar su su shiga, amma daga dawowarsu aka tsare wasu daga cikinsu bisa zargin karya dokar da ta ayyana yankin a matsayin “yankin soji da aka rufe”.

Magajin garin Qusra, Abdel Azim Wadi, ya ce sojojin Isra’ila na hana isar da muhimman kayayyaki ga iyalan uku da suka makale a yankin.

A nasa bangaren, Ambasadan Amurka a Isra’ila, Mike Huckabee, ya yi gargadin cewa hare-haren da ‘yan share wuri ke kai wa Falasɗinawa na lalata martabar Isra’ila a idon duniya.

Ya ce Isra’ila na bukatar abokai da yawa, don haka bai kamata ta ci gaba da samar wa kanta ƙarin makiya ba.

0 $type={blogger}: