Wasu ’yan’uwa mata uku daga gida ɗaya sun mutu bayan jirgin ruwan da suke ciki ya kife a Dam ɗin Tiga da ke ƙaramar hukumar Tudunwada ta Jihar Kano.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana ranar Asabar, kamar yadda wasu ’yan uwan mamatan suka bayyana.
An bayyana sunayen mamatan da Murjanatu da Atikatu da Bilkisu, wadda aka fi sani da Amira. Dukkansu ’yan asalin ƙauyen Yalwan Rugu-Rugu ne.
Shugabar ƙaramar hukumar Tudunwada kuma shugabar ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta ALGON a Jihar Kano, Hajiya Sa’adatu Salisu Soja, ta tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa.
Ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da al’ummar Yalwan Rugu-Rugu bisa wannan mummunan lamari.
Ta ce: “Muna miƙa ta’aziyyarmu ta gaskiya ga iyalan mamatan da al’ummar Yalwan Rugu-Rugu bisa wannan babban rashi mai raɗaɗi.”
Hajiya Sa’adatu ta kuma yi addu’ar Allah Ya gafarta wa mamatan, Ya jiƙansu, Ya ba su rahama, sannan Ya bai wa iyalansu ƙarfin jure wannan babban rashi.
Ya zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto, rundunar ’yan sandan Jihar Kano da Hukumar Kashe Gobara ta jihar ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ko ayyukan ceto ba.
Tags
Labarai
