Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Talata a matsayin ranar hutun Maulidi.

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Talata a matsayin ranar hutun Maulidi.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 25 ga Agusta, 2026, a matsayin ranar hutu ta ƙasa domin bikin Eid-ul-Mauludi, wato ranar tunawa da haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin Gwamnatin Tarayya. Sanarwar, wadda Babbar Sakatare ta Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dr. Magdalene Ajani, ta sanya wa hannu, ta fito ne a ranar Juma’a.

Ministan ya taya Musulmin Najeriya da ma waɗanda ke zaune a ƙasashen waje murnar wannan rana, tare da kira gare su da su yi tunani kan kyawawan halayen Annabi Muhammad (SAW), musamman tausayi, tawali’u da hidima ga al’umma.

Tunji-Ojo ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’ar samun zaman lafiya da haɗin kan ƙasa, yana mai cewa kiyaye haɗin kai nauyi ne da ya rataya a kan kowa.

Ya bukaci ‘yan ƙasa da su gudanar da bukukuwan cikin natsuwa, lumana da mutunta juna, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Saboda wannan sanarwa, ma’aikata a faɗin Najeriya za su samu hutun aiki a ranar Talata, 25 ga Agusta, domin bikin Eid-ul-Mauludi na 2026/1448.

0 $type={blogger}: