Babban lauya mai rajin kare hakkin bil'adama, Femi Falana (SAN), ya bukaci tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), da ya nemi afuwar 'yan Najeriya tare da yin murabus daga mukaminsa na Shugaban Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa (National Peace Committee) saboda kalamansa na cewa marigayi Janar Sani Abacha bai wawure dukiyar Najeriya ba.
A cikin wata sanarwa mai taken "Re: Abdulsalami Abubakar: Abacha Never Looted Treasury," Falana ya ce kalaman Abdulsalami wani yunkuri ne na sauya tarihin abin da ya faru a zamanin mulkin Abacha.
Falana ya bayyana cewa gwamnatin Abdulsalami ce da kanta ta kafa Kwamitin Bincike na Musamman (Special Investigation Panel) a shekarar 1998 domin binciken zargin cin hanci da karkatar da kudaden gwamnati a lokacin mulkin Abacha.
A cewarsa, binciken ya gano yadda aka karkatar da makudan kudade tare da taimakon wasu jami'an Babban Bankin Najeriya (CBN), lamarin da ya sa gwamnatin Abdulsalami ta fitar da Dokar Kwace Kadarori ta 1999 (Forfeiture of Assets Decree No. 53) wadda ta ba gwamnati damar kwace kadarorin da aka ce an mallaka ta haramtacciyar hanya daga Abacha da iyalansa da abokan huldarsa.
Falana ya ce an kwato daruruwan miliyoyin daloli da fam da kudaden Deutsche Mark da kadarori da motocin alfarma, kuma dokar ta bayyana cewa an samu wadannan kadarori ne ta hanyar cin hanci da rashawa.
Ya kuma yi watsi da ikirarin Abdulsalami cewa kudaden an adana su ne domin kare Najeriya daga takunkumin kasashen waje bisa shawarar tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi da tsohon shugaban Benin Mathieu Kérékou.
Falana ya ce babu wata kotu a Najeriya ko kasashen waje da ta taba amincewa cewa kudaden da aka kwato na gwamnati ne da aka ajiye bisa ka'ida. Ya kara da cewa gwamnatocin tsoffin shugabanni Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan, da Muhammadu Buhari sun ci gaba da kwato biliyoyin daloli daga kadarorin da ake alakanta da Abacha.
A karshe, Falana ya bukaci Janar Abdulsalami Abubakar ya janye kalamansa, ya ba 'yan Najeriya hakuri, sannan ya yi murabus daga shugabancin Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa, yana mai cewa kalaman nasa sun rage amincewar jama'a da mutuncinsa.

0 $type={blogger}:
Post a Comment