Ƙasar Belgium ta lallasa mai masaukin baki Amurka da ci 4-1, inda ta samu nasaran kaiwa wasan dab dana kusa da na ƙarshe (kwata fainal) na Gasar cin Kofin Duniya na 2026.
Charles De Ketelaere ne ya zama gwarzon wasan bayan da ya zura ƙwallaye biyu, wanda ya taimaka wa Belgium ta mamaye wasan tun daga farkonsa.
Ya fara jefa ƙwallo a raga da wuri, kafin Malik Tillman ya rama wa Amurka ta bugun daga kai sai mai tsaron gida. Sai dai De Ketelaere ya sake zura ta biyu cikin kankanin lokaci, ya mayar da Belgium kan gaba.
A zagaye na biyu, kuskuren mai tsaron ragar Amurka Matt Freese ya bai wa Hans Vanaken damar ƙara ta uku cikin sauƙi, kafin tsohon ɗan wasan gaba Romelu Lukaku ya tabbatar da nasarar Belgium da ƙwallo ta huɗu a ƙarshen wasan.
Kafin fara wasan, an yi ta ce-ce-ku-ce kan dawowar Folarin Balogun bayan FIFA ta janye dakatarwar wasa ɗaya da aka yi masa. Duk da haka, kasancewarsa cikin tawagar Amurka bai hana Belgium samun gagarumar nasara ba.
Amurka ta yi ƙoƙarin dawo wa cikin wasan a karo na biyu, amma ta kasa amfani da damar da ta samu. Haka kuma, kyaftin ɗin ƙungiyar Christian Pulisic ya ji rauni, lamarin da ya ƙara dagula wa masu masaukin baki al'amura.
Da wannan sakamakon, Belgium za ta kara da Spain a wasan kusa da na ƙarshe, yayin da Amurka ta fice daga gasar tare da sauran ƙasashen da suka karɓi baƙuncin gasar, wato Canada da Mexico.

0 $type={blogger}:
Post a Comment