Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya yaba wa rundunar sojin Najeriya bisa nasarar ceto mutane 360 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a tsaunukan Mandara.
Rahotanni sun nuna cewa an ceto mutanen ne—maza, mata da yara—a wani farmaki na hadin gwiwa da sojojin Operation Hadin Kai suka gudanar a kudancin jihar Borno.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, Gwamna Zulum ya bayyana aikin a matsayin “babbar bajinta da nuna jarumtaka da kwarewa,” yana mai cewa hakan na nuna ci gaban amfani da bayanan sirri wajen yaki da ta’addanci a Arewa maso Gabas.
Zulum ya kuma gode wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da shugabannin soji, da dakarun da suka shiga aikin ceto, yana mai cewa jajircewarsu ya sake kawo fata ga al’ummomin da abin ya shafa.
Ya kuma bukaci mazauna yankin da su ci gaba da zama cikin shiri tare da ba hukumomin tsaro hadin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen ci gaba da murkushe ‘yan ta’adda.
Gwamnan ya sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa sojoji ta hanyar kayan aiki da hadin gwiwa domin tabbatar da dawowar zaman lafiya mai ɗorewa a jihar Borno.
A halin yanzu, rahotanni sun ce ana ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro a yankin domin kawar da ragowar cibiyoyin ‘yan ta’adda.

0 $type={blogger}:
Post a Comment