Wasu Gungun Mutane Sun Kona Wata Mata Har Lahira a Kaduna Bisa Zarginta da Satar Yara da Ba a Tabbatar ba.

Wasu Gungun Mutane Sun Kona Wata Mata Har Lahira a Kaduna Bisa Zarginta da Satar Yara da Ba a Tabbatar ba.

Wata mata ta rasa ranta bayan wasu gungun mutane sun lakada mata duka tare da kona ta a garin Maraban Jos da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna, bisa zargin cewa tana ƙoƙarin satar yara.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, inda ya jawo tashin hankali a yankin, yayin da mazauna garin suka ce jita-jitar satar yara ta haifar da fargaba da shakku tsakanin jama’a.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa matar, wadda aka ce matar aure ce kuma uwa ce, tana kan hanyarta zuwa wajen karatun addini ne lokacin da wasu matasa suka zarge ta da yunƙurin satar yara.

Bayan zargin ya bazu cikin al’umma, jama’a da dama sun taru suka far mata da duka kafin jami’an tsaro su isa wurin.

An ceto matar tare da kai ta ofishin ‘yan sanda domin kare lafiyarta da gudanar da bincike.

Sai dai lamarin ya ƙara tsananta yayin da ɗaruruwan matasa suka mamaye ofishin ‘yan sandan suna neman a basu matar. 
Rahotanni sun ce sun rinjayi jami’an tsaro, inda suka fitar da ita daga hannunsu sannan suka banka mata wuta.

A yayin rikicin, ‘yan sanda sun yi harbe-harben gargadi domin tarwatsa jama’ar, inda aka ruwaito an harbi wani matashi tare da jikkata wasu.

Wani mazaunin yankin ya bayyana takaicinsa, yana mai cewa ya kamata a bar jami’an tsaro su gudanar da bincike maimakon jama’a su ɗauki doka a hannunsu.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce zargin da aka yi wa matar “ƙarya ce ta satar yara ba tare da hujja ba.”

Ya ce jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar ceto matar da farko, amma daga baya gungun mutanen suka mamaye ofishin, suka kwace ta, suka kashe ta sannan suka kona gawarta.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana lamarin a matsayin babban laifi da cin zarafin doka.

An kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin, yayin da ake ci gaba da neman wasu da suka tsere.

‘Yan sanda sun ce an fara cikakken bincike kuma duk wanda aka samu da hannu zai fuskanci hukunci.

0 $type={blogger}: