Shugabannin Musulmi da mabiya addinin Musulunci daga sassa daban-daban na Jihar Oyo sun taru a filin addu’a na Yidi da ke Agodi, Ibadan, domin neman taimakon Allah game da karuwar matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane da fashi da makami da sauran ayyukan ta’addanci a jihar.
Taron addu’ar, wanda aka gudanar da amincewar Babban Limamin Ibadan, Abdulganiy Agbotomokekere, ya samu halartar malamai da shugabannin al’umma da daruruwan mabiya daga kananan hukumomi 11 na yankin Ibadan.
Masu jawabi a wajen taron sun jaddada cewa hadin kai tsakanin ‘yan Najeriya, tare da yawaita addu’o’i, na daga cikin manyan hanyoyin da za su taimaka wajen shawo kan matsalolin rashin tsaro da ke addabar kasar.
Malam Muyideen Onihantu, wanda ya gabatar da lakca a taron, ya ce manufar addu’ar ita ce neman taimakon Allah domin kawo karshen rashin tsaro da ya hana jama’a zaman lafiya.
Ya bayyana cewa taron ba na kabilar Yarbawa kadai ba ne, domin mambobin al’ummomin Hausawa da Nufawa da Tapa ma sun halarta, abin da ya nuna muhimmancin hadin kai wajen magance matsalolin tsaro.
Shi ma Babban Limamin Sabo, Ibrahim Abdullahi, ya bukaci gwamnati ta kara kaimi wajen kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su tare da inganta matakan tsaro domin dakile irin wadannan hare-hare.
A nasa bangaren, Sakatare Janar na Kungiyar Musulmin Jihar Oyo, Abidemi Siyanbade, ya nuna damuwa kan yadda ‘yan bindiga ke kara kutsawa yankunan jihar, yana mai gargadin cewa idan ba a dauki matakin gaggawa ba, matsalar na iya bazuwa zuwa sauran yankunan Kudu maso Yamma.
Ya kuma yi watsi da ikirarin cewa masu aikata wadannan laifuka suna da alaka da addinin Musulunci, yana mai cewa su masu laifi ne kawai da ke haddasa rashin zaman lafiya a kasa.
Siyanbade ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rika bai wa jami’an tsaro bayanan sirri kan duk wani abu da suka gani na zargi a yankunansu, yana mai cewa tabbatar da tsaro nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa.
Shugaban dalibai Muslim na Najeriya, Mustafa Olumide, ya ce dalibai na daga cikin wadanda matsalar rashin tsaro ta fi shafa. Ya gargadi cewa idan ba a dakatar da garkuwa da mutane ba, iyaye da dama za su fara cire ‘ya’yansu daga makarantu saboda fargabar tsaro.
A karshe, shugabannin Musulmin sun yi addu’ar samun nasarar kubutar da duk wadanda ke hannun masu garkuwa da mutane tare da dawowar zaman lafiya da tsaro a Jihar Oyo da Najeriya baki daya.

0 $type={blogger}:
Post a Comment