Isra'ila Ta Kai Harin Ramuwar Gayya Kan Iran Bayan Harin Makamai Masu Linzami da Iran ta Kai cikin Israi'la.

Isra'ila Ta Kai Harin Ramuwar Gayya Kan Iran Bayan Harin Makamai Masu Linzami da Iran ta Kai cikin Israi'la.

Isra'ila ta kaddamar da hare-haren sama kan wasu wuraren soji a yammaci da tsakiyar Iran bayan Iran ta harba jerin makamai masu linzami zuwa arewacin Isra'ila, lamarin da ya kara tsananta rikicin da ke tsakanin kasashen biyu tun bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a watan Afrilu.

Sojojin Isra'ila sun bayyana cewa jiragen yakinsu sun kai hare-hare kan wuraren soji da suka danganta da hukumomin tsaron Iran. Rahotanni sun ce an ji karar fashe-fashe a Tehran da Isfahan da Tabriz da kuma yankunan da ke kusa da Karaj. 
Sai dai hukumomin Iran sun ce ba a kai hari kan unguwannin birnin Tehran ba, kuma babu rahoton asarar rayuka nan take.

Rikicin ya kara kamari ne bayan rundunar Kare juyin juya halin Musulunci ta Iran, IRGC ta harba makamai masu linzami zuwa arewacin Isra'ila, inda ta bayyana harin a matsayin farkon jerin hare-haren da za su ci gaba har na tsawon mako guda. 
Israi'la ta Yi Ikirarin cewwa tsarin kariyar sararin samaniyarta ya yi nasarar kakkabo mafi yawan makaman, sannan daga baya aka ba mazauna yankunan da abin ya shafa damar fita daga mafaka.

Tashin hankalin ya biyo bayan hare-haren da Isra'ila ta kai kan wuraren da take zargin na Hezbollah ne a kudancin Beirut a ranar Lahadi. 
Iran ta gargadi cewa duk wani sabon hari da za a kai kan Lebanon ko muradunta zai fuskanci martani mai tsauri.

A halin da ake ciki, Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci bangarorin su nuna hakuri tare da kauce wa kara rura wutar rikici. Rahotanni sun ce ya tattauna da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, inda ya bukace shi da kada ya mayar da martani domin kada hakan ya kawo cikas ga kokarin diflomasiyya da ake yi.

Sabon tashin hankalin ya kuma yi tasiri ga harkokin tsaro da tattalin arziki a yankin. 
Iran ta dakatar da dukkan jiragen da ke shigowa Filin Jirgin Sama na Imam Khomeini da ke Tehran, yayin da farashin danyen mai ya tashi sakamakon fargabar katse hanyoyin samar da makamashi daga Gabas ta Tsakiya.

Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da dama sun yi kira ga bangarorin da su rage zafin rikicin tare da komawa teburin tattaunawa, suna gargadin cewa ci gaba da hare-haren juna na iya jefa yankin cikin wani babban rikici mai fadin gaske.

0 $type={blogger}: