Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ce ta kaddamar da wani hari da makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan sansanonin sojin Amurka guda takwas a yankin, tana bayyana harin a matsayin “martani mai tsauri” ga abin da ta kira sabbin hare-haren da aka kai wa Iran.
A cikin wata sanarwa, IRGC ta ce rundunar sojinta na ruwa da kuma bangaren sararin samaniya ne suka gudanar da aikin da sanyin safiyar Lahadi. Ta ce daga cikin wuraren da aka nufa akwai sansanin sojin Amurka na Ali Al Salem da ke Kuwait da kuma hedikwatar Rundunar Sojan Ruwa ta Amurka ta Fifth Fleet a Salman Port, Bahrain.
IRGC ta bayyana cewa an yi amfani da makamai masu linzami masu tafiya mai nisa da jirage marasa matuka wajen kai harin, tare da ikirarin cewa an lalata wuraren da aka kai wa hari.
Rundunar ta ce wannan martani ya biyo bayan hare-haren da Amurka ta kai kan wasu wuraren tsaron gabar tekun Iran guda biyar a baya.
Har ila yau, IRGC ta yi gargadi kan batun zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar ruwan Hormuz, inda ta ce duk wani jirgin da ya karya ka’idojin da aka gindaya zai fuskanci mataki mai tsauri.
Wannan sabon tashin hankali ya biyo bayan rahoton Rundunar Tsakiyar Amurka (CENTCOM) cewa ta kai wasu hare-hare kan wurare a cikin Iran bayan wani lamari da ya shafi wani jirgin dakon mai.
Kafofin watsa labaran Iran sun bayar da rahoton fashe-fashe a lardin Hormozgan da kuma tsibirin Qeshm, amma ba a samu cikakken bayani kan wuraren da lamarin ya faru da kuma barnar da aka yi ba.
Amurka da Iran na ci gaba da zargin juna kan karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta, yayin da rikici ke kara tsananta a yankin.

0 $type={blogger}:
Post a Comment