Gwamnatin Tarayya Ta Fitar Da Naira Biliyan 32.8 Don Inganta Ayyukan Lafiya Na Farko A Fadin Najeriya


Gwamnatin Tarayya Ta Fitar Da Naira Biliyan 32.8 Don Inganta Ayyukan Lafiya Na Farko A Fadin Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta amince da fitar da Naira biliyan 32.8 ga jihohi karkashin shirin Basic Health Care Provision Fund (BHCPF) na kashi na biyu na shekarar 2026, domin ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya na matakin farko, inshorar lafiya, shirin dakile barkewar cututtuka da ayyukan gaggawa a fadin Najeriya.

Ministan Kula da Lafiya da Jin Dadin Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan bayan taron kwamitin sa ido kan shirin BHCPF karo na 15.

Ya ce wannan sabon tallafin zai taimaka wajen ci gaba da gyaran tsarin lafiya da kuma fadada samun ingantaccen magani ga jama’a.

Ministan ya bayyana cewa daga cikin Naira biliyan 339 da aka raba ta hanyar BHCPF cikin shekaru 12 da suka gabata, an fitar da Naira biliyan 235 a cikin shekaru uku da suka gabata karkashin gwamnatin yanzu.

Ya ce sama da cibiyoyin lafiya na farko 1,000 a jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja suna samun tallafin kowane wata uku domin inganta ayyukan kiwon lafiya da inshora da magance matsalolin gaggawa.

Farfesa Pate ya kara da cewa tallafin ya taimaka wajen kara amfani da asibitoci, inda sama da ’yan Najeriya 130,000 suka amfana da ayyukan gaggawa da shirin ya dauki nauyi.

Ya bayyana cewa jihohi 35 sun kafa tsarin ayyukan gaggawa na lafiya, yayin da jihohin Benue da Imo ke amfani da cibiyoyin lafiya na gwamnatin tarayya.

Dangane da dakile cututtuka, ministan ya ce kudaden sun taimaka wajen karfafa cibiyar dakile cututtuka ta Najeriya (NCDC) wajen gano barkewar cututtuka da daukar matakan gaggawa.

Ya kuma ce an fitar da karin kudaden gaggawa ga dukkan jihohi 36 domin shiryawa yiwuwar barkewar cutar Ebola, sakamakon rahoton bullar cutar a wasu kasashen Afirka, duk da cewa Najeriya ba ta samu rahoton bullar cutar ba.

Ministan ya bayyana cewa an gyara sama da cibiyoyin lafiya na farko 3,000 zuwa matakin inganci na biyu, yayin da kusan 1,000 ke kan matakan gyara daban-daban.

Ya bukaci gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi su biya kudaden tallafin da ake bukata, domin hakan zai kara yawan kudaden da ake samu wajen gudanar da ayyukan lafiya.

Haka kuma ya bayyana cewa sama da mutane miliyan shida ne suka shiga tsarin inshorar lafiya cikin shekaru uku da suka gabata.

Ya kara da cewa sama da mata 48,000 sun samu kulawar gaggawa kyauta ta bangaren haihuwa, ciki har da tiyatar haihuwa, yayin da cibiyoyin lafiya 207 ke bayar da maganin matsalar yoyon fitsari (fistula) kyauta.

0 $type={blogger}: