Gwamnatin jihar Kano Za Ta Fara Gwajin Lafiya Ga Ma’aurata 3,000 Kafin Shirin Auren Gata.

Gwamnatin jihar Kano Za Ta Fara Gwajin Lafiya Ga Ma’aurata 3,000 Kafin Shirin Auren Gata.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kammala shirye-shiryen gudanar da gwajin lafiya ga ma’aurata 3,000 da suka yi rajista domin shiga shirin auren gata da gwamnatin jihar ke shiryawa.

Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Sheikh Mujahedeen Aminudeen, ya bayyana cewa za a fara gudanar da gwajin ne daga ranar Litinin, 8 ga Yuni, 2026, a kananan hukumomi 24 na jihar.

A cewarsa, ma’auratan sun hada da mata 1,500 da maza 1,500, kuma za a yi musu gwaje-gwaje domin tantance lafiyarsu kafin a daura musu aure.

Ya ce an shirya gudanar da gwajin ne tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano da Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Jihar Kano.

Gwaje-gwajen da za a yi sun hada da na cutar HIV/AIDS da hepatitis B  da tantance jinsin halitta (genotype) da amfani da miyagun kwayoyi da ciwon sanyi (gonorrhoea) da sauran cututtukan da ake dauka ta hanyar jima’i.

Aminudeen ya ce an umurci duk wadanda suka yi rajista da su je ofisoshin Hisbah da ke kananan hukumominsu domin gudanar da gwajin, yana mai gargadin cewa duk wanda bai halarta ba za a cire sunansa daga cikin wadanda za su amfana da shirin.

Ya kara da cewa wadanda suka samu sakamakon gwaji mai gamsarwa ne kawai za su cancanci shiga cikin shirin auren.

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta sake dawo da shirin auren gata domin taimaka wa marasa karfi wajen yin aure da kuma rage wasu matsalolin zamantakewa da suka hada da karuwanci da sauran dabi’u marasa kyau a tsakanin matasa.

0 $type={blogger}: