Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Aminu Gwarzo, ya bayyana alhininsa kan rasuwar fitaccen dan jarida kuma tsohon shugaban kafafen yada labarai na gwamnati, Alhaji Adamu Getso.
Rahotanni sun ce Getso ya rasu ne a ranar Asabar a garinsa na Getso da ke karamar hukumar Gwarzo a jihar Kano.
Marigayin ya taba zama Manajan Darakta na gidan Talabijin din Abubakar Rimi (ARTV), sannan ya kuma rike mukamin Manajan Darakta na Radiyon jihar Kano a wa’adin mulki na biyu na tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.
A cikin sakon ta’aziyya da kakakinsa Ibrahim Shuaibu ya fitar a ranar Lahadi, Gwarzo ya bayyana marigayin a matsayin gogaggen dan jarida kuma kwararren mai yada labarai wanda gudunmawar da ya bayar wajen bunkasa harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a a Kano za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa.
Ya ce Adamu Getso ya sadaukar da wani babban bangare na rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima ta hanyar aikin yada labarai, inda ya bar kyakkyawan tarihi na kwarewa da rikon amana da jajircewa wajen bautar jama’a.
Gwarzo ya ce rasuwar tasa babban rashi ne ba ga iyalansa kadai ba, har ma ga daukacin al’ummar Kano da kuma bangaren yada labarai baki daya.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus, sannan Ya bai wa iyalansa da masoyansa hakurin jure wannan babban rashi.

0 $type={blogger}:
Post a Comment