Hukumomin ‘yan sanda a Italiya sun kama wasu ‘yan Nijeriya biyu tare da wasu mutum uku daga ƙasashen waje bisa zargin yin garkuwa da kuma yi wa wata ‘yar yawon bude ido ‘yar ƙasar Kolombiya fyade a birnin Rome.
Wadanda ake zargin, Isibor Wisdom mai shekara 29 da Paul Nwabueze mai shekara 39, an kama su tare da wasu mutum uku daga Gambia da Mali. Dukkan su na tsare yayin da bincike ke ci gaba.
Rahotanni daga ‘yan sanda sun bayyana cewa matar mai shekaru 32 an ce an yaudare ta ne a ranar 19 ga Mayu daga wani gidan cin abinci, inda wani mutum ya ce zai sayar mata da hodar wiwi.
Bayan an lallaba ta ta bi shi, an kai ta wani gini da aka watsar a wajen birnin Rome, inda aka rike ta tsawon kusan kwanaki uku.
Hukumomi sun ce ana zargin an ci zarafinta kuma an yi mata fyade akai-akai tare da yi mata barazana a lokacin da take tsare.
Daga bisani, matar ta samu nasarar tserewa daga wurin, inda wani mai wucewa ya tarar da ita cikin mawuyacin hali ya kuma kira jami’an agaji.
Bayan haka ne ‘yan sanda suka kai samame a ginin, inda suka kama wadanda ake zargin. A halin yanzu ana ci gaba da bincike domin kamo sauran wadanda ake zargi da hannu a lamarin, ciki har da wanda ya yaudari matar da direban da ya kai ta wurin.
Ana tuhumar su da manyan laifuka da suka shafi fyade da kuma cin zarafin mutum, yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike.

0 $type={blogger}:
Post a Comment