Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar sun halarci sallar Idi tare da Musulmai a wurare daban-daban a Najeriya.
Tinubu ya halarci sallar Idi a Dodan Barracks da ke Lagos tare da manyan jami’an gwamnati da jami’an tsaro.
A Abuja kuma, Atiku Abubakar ya yi sallar Idi a Masallacin AYA, inda ya nuna godiya ga Allah tare da kiran ‘yan Najeriya su rungumi zaman lafiya da haɗin kai da tausayi.
Dukkan shugabannin sun yi kira ga ‘yan ƙasa da su ƙara ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya, musamman yayin da ƙasar ke shiga sabon yanayin siyasa.

0 $type={blogger}:
Post a Comment