An samu girgizar kasa mai karfin maki 5 a kusa da birnin Turpan da ke yankin Xinjiang na arewa maso yammacin kasar China a ranar Juma’a, kamar yadda cibiyar kula da girgizar kasa ta China ta bayyana.
Rahotanni sun ce girgizar ta faru ne da misalin karfe 2:55 na rana agogon kasar China (0655 GMT).
Har zuwa yanzu babu rahoton asarar rayuka ko barnar da girgizar ta haddasa, yayin da hukumomi ke ci gaba da bibiyar lamarin.
Birnin Turpan na daya daga cikin yankunan da ake yawan samun girgizar kasa saboda yanayin kasa da yankin yake ciki.
Hukumomin kasar China sun ce jami’an agaji da masu aikin gaggawa suna cikin shiri domin duba ko akwai wata illa da girgizar ta haifar ko kuma yiwuwar sake afkuwar wata girgizar bayan wannan.

0 $type={blogger}:
Post a Comment